in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Turai sun bukaci Rasha da ta janye sojojinta daga Crimea
2014-03-09 17:29:10 cri
A Jiya ne shugaban kasar Amurka Barack Obama ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Burtaniya, Faransa, Italiya, Latvia, Lithuania, Estonia ta wayar tarho dangane da yanayin da ake ciki a kasar Ukraine.

Shugabannin kasashen bakwai sun yi kira ga kasar Rasha da ta janye sojojinta da ta tura zuwa yankin Crimea a karshen watan Fabrairu,kana ta bar masu sa ido na kasa da kasa da masu kare hakkin dan Adam su shiga yankin na Crimea. Daga bisani kuma, kasashen bakwai sun bukaci kasar Rasha da ta kafa wata tawagar da za ta tattauna da kasar Ukraine kai tsaye ta yadda za a sasauta yanayin da ake ciki a halin yanzu, da kuma kiyaye iko da cikakken yankin kasar Ukraine. Bugu da kari, kasashen bakwai sun yi gargadi cewa, idan kasar Rasha ba za amsa bukatun kasashen bakwai dangane da batutuwan da suka ambata ba, kasashen Amurka da Turai za su kakaba wa kasar Rasha takunkumi.

Dangane da lamarin, ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana a ranar Asabar cewa, ba kasar Rasha ba ce ta haddasa rikicin kasar Ukraine, kuma kasar Rasha ta sha yin gargadi ga kasar Ukraine dangane da rikicin kasar amma a karshe rikici ya barke a kasar ta Ukraine. Kasar Rasha ta amince da yin shawarwari tare da kasashe yammacin don neman hanyoyin warware rikicin kasar Ukraine cikin hadin gwiwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China