in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanukovich zai yi jawabi a Rasha
2014-03-10 20:45:22 cri
A yau ranar Litinin ne, muhimman kafofin yada labaru na kasar Rasha, ciki had da kamfanin dillancin labaru na Itar-tass suka jiyo daga bakin na hannun daman Victor Yanukovich na cewa, mista Yanukovich, wanda majalisar dokokin kasar Ukraine ta tube shi daga mukamin shugaban kasar, zai yi jawabi a birnin Rostov-on-Don da ke kudancin kasar Rasha a ranar 11 ga wata. Kuma ba da jimawa ba za a bayyana lokaci da kuma wurin da zai yi jawabin.

A ranar 28 ga watan jiya ne mista Yanukovich ya fito a fili a Rostov-on-Don, inda ya bayyana ra'ayinsa kan halin da Ukraine ke ciki a wani taron manema labaru, kuma a cewarsa, shi ne halataccen shugaban kasar ta Ukraine. Kuma majalisar dokokin Ukraine ta zartas da kudurin tube shi daga mukaminsa ne ba bisa doka ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China