Turchinov wanda ya bayyana hakan a jiya Jumma'a 7 ga watan nan,
ya kara da cewa waccan shawara, ta keta jerin ka'idojin kundin tsarin mulkin kasar Ukraine. A cewar sa bisa tsarin mulkin kasar, Ukraine ce ke da cikakken iko da dukkanin fadin kasar, kuma babu wanda zai iya kwace wani yankin kasar.
Ya kara da cewa yankin Crimea mai cin gashin kansa, wani kashi ne da ba za a iya ballewa daga Ukraine ba. don haka kuri'ar raba gardama kan batun ficewar Crimea daga kasar, za ta zamo halastacciya ce kadai, idan har aka gudanar da ita a dukkanin fadin kasar ta Ukraine.
Har wa yau dai wannan rana, shi ma wani mai magana da yawun babban magatakardar MDD ya bayyana cewa, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarori daban daban da wannan batu ya shafa, da su kai zuciya nesa domin kaucewa abin da kaje ya zo. (Fatima)