in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanukovich zai sake ganawa da manema labaru
2014-03-11 16:49:34 cri
Shugaban kasar Ukraine da majalisar kasar ta tube shi daga mukaminsa Victor Yanukovich zai kira taronsa na ganawa da manema labaru na 2 bayan da ya bar kasarsa ta Ukraine, a yammacin ranar 11 ga wata, bisa agogon Moscow.

An ce za a gudanar da taron a wata cibiyar nune-nune na garin Rostov-on-Don dake kudu maso yammacin kasar Rasha. Ta la'akari da yanayin zaman dar-dar da ake ciki a gabashin kasar Ukraine gabanin jefa kuri'ar raba gardamar da zai gudana a yankin Crimea a ranar 16 ga wata, wane irin furuci ne shi Yanukovich zai bayyana kan batun ya zama abun dake janyo hankulan kafofin yada labaru. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China