Wani kakakin kamfanin samar da wutar lantarki wanda ya bayyana haka a ran 14 ga wata cewa ya yi, jihar Xinjiang ta yi amfani da albarkatun hasken rana a wurin domin samar da wutar lantarki, sakamakon haka, manoma da makiyaya kimanin dubu 30 a wurin sun fara amfani da wutar lantarki yanzu.
A nasa bangaren, wani jami'i mai kula da harkokin samarwa manoma wutar lantarki na jihar ya nuna cewa, yawan mutanen da ba su da wutar lantarki kimanin dubu 460 suna kauyuka, ya zuwa karshen shekarar 2014, kamfanin zai samu damar warware wannan matsala, lamarin da zai zama shekara guda kafin lokacin da aka kayyade a baya, kana yawan kudin da za a zuba domin wannan aiki zai kai RMB biliyan 2 da wani abu. (Amina)