Wata sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce harin ta'addancin da ya kai ga kisan ma'aikatan gwamnati da mutanen da ba su san hawa ba balle sauka, wani yunkuri na kawo rashin zaman lafiya da hadin kai tsakanin kungiyoyin kabilu da na addinai dabam-dabam da ke zaune a yankin.
Kakakin kungiyar wanda ba a bayyana sunansa ba cikin sanarwar kungitar, ya bayyana kudurin dukkan kungiyoyin kabilu na yaki da ayyukan ta'addanci, kana sun goyi bayan kokarin gwamnati na yaki da ayyukan ta'addanci kamar yadda doka ta tanada. (Ibrahim)