in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsawon hanyar jirgin kasa ta jihar Xinjiang ta karu zuwa kilomita 4479
2012-02-07 16:28:48 cri

Kwanan baya hukumar zirga-zirgar jiragen kasa ta birnin Wulumuqi na jihar Xinjiang wani yanki mai cin gashin kanta a kasar Sin, ta fayyace cewa, a shekara ta 2011, jihar Xinjiang ta gaggauta shimfida hanyar jiragen kasa. A yanzu, tsawon hanyar jiragen kasa ta jihar Xinjiang ta karu daga tsawon kilomita 2819 na shekara ta 2008 zuwa kilomita 4479.

Bisa labarin da aka bayar, a shekarar 2011, yawan kudin da aka ware kan aikin shimfida hanyar jiragen kasa a jihar Xinjiang ya kai kudin Sin RMB ko kuma Yuan biliyan 11 da miliyan 600. Yawan fasinjojin da jiragen kasa suka yi jigilarsu ya kai miliyan 40, abun da ya kafa wani sabon tarihi. Kana yawan kayayyakin da aka fitar zuwa waje ta hanyar jiragen kasa a jihar ya kai ton miliyan 2 da dubu 475, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari.

An kiyasta cewa, zuwa shekara ta 2015, tsawon hanyar jiragen kasa ta jihar Xinjiang zai kai kilomita 8200.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China