in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfin samar da wutar lantarki da iska a jihar Xinjiang zai kai kilowatt miliyan 11
2011-10-05 19:48:25 cri
A kwanakin baya ne, gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur ,da ke arewa maso yammacin kasar Sin, ta ba da izini ga wasu yankunan jihar guda 5 su kara bunkasa ayyukan samar da wutar lantarki ta amfani da karfin kadewar iska. Gwamnatin ta ce ta amfani da wannan salo adadin yankunan da gwamnatin jihar ta yarda da su wajen bin wannan tsari za su kai 12, wadanda kuma karfin wutar da za su samar zai kai kilowatt miliyan 11. Daukar wannan mataki tamkar aza wani harsashi ne mai kyau ga shirin amfani da karfin iska yadda ya kamata, domin bunkasa ayyukan samar da wuta da karfin iska a bisa wani kayyadaden tsari.

An ce, yawan karfin iska da jihar Xinjing ke da shi ya kai kilowatta miliyan 8900, wanda ya kasance kashi 20.4% cikin dukkanin karfin iska da ake da shi a fadin kasar Sin, hakan ya tabbatar da matsayin jihar na wata babbar cibiyar samar da makamashi da ke iya sabuntawa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China