Jiya Alhamis 25 ga wata a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, an gudanar da bikin murnar babbar Salla. Inda wakilan bangarori daban-daban na jihar su yi taru.
A gun bikin, sakataren kwamitin JKS na jihar Zhang Chunxian ya ce, ya zuwa yanzu, jihar ta samu ci gaba sosai a fannoni daban-daban, ciki har da tattalin arziki, zamantakewar al'umma, hadin gwiwa tsakanin a'ummomin kabilu daban-daban. A fannin tattalin arziki, daga watan Jarairu zuwa Satumba na shekarar bana, yawan GDP da jihar ta samu ya kai kudin Sin RMB biliyan 502.2 wanda ya karu da kashi 11.5 cikin dari idan an kwatanta shi da na bara war haka, wanda kuma ya fi na dukkan kasar yawa da kashi 3.8 bisa dari. A bangaren zamantakewar al'umma, a cikin shekaru uku da suka gabata, yawan kudin da jihar ta kashe a wannan fanni ya kai kashi 70 bisa dari na dukkan kudin da aka kashe, kuma an ci gaba da kyautata zaman rayuwar jama'a.
Babbar Salla kuma a kan kira ta bikin yanke dabbobi, wadda ta kasance muhimmiyar biki ga musulmai a duniya. (Amina)