A ran 6 ga wata, an yi bikin fara gina asibiti na farko na warkar da ciwace-ciwacen tsoffi a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Bayan da aka kammala ginin, tsoffi miliyan 2 da dubu 340 na jihar za su ci gajiyar wannan asibiti.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan asibiti ya zama daya daga cikin ayyuka mafi muhimmanci na jihar Xinjiang a shekarar 2011, yawan kudin da aka ware domin gina asibitin ya kai kudin Sin RMB miliyan 120. Fadin gine ginen da za a gina a matakin farko zai kai muraba'in mita dubu 45, inda za a sanya gadoji kimanin 500, daga bisani, yawan gadojin da za a sanya cikin asibitin zai kai dubu 1 bayan da aka kammala gina gine-gine a matakai na biyu da na uku.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan tsoffi na jihar Xinjiang ya kan karu da kashi 4.36 cikin dari a kowace shekara, wannan adadi ya fi matsakaicin matsayin yawan tsoffi a kasar Sin.(Lami)