Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a kyautata filaye da dakuna da kayayyaki dake makarantun kauyuka a yanzu, tare da kara wasu sabbin kayayyaki, domin kafa cibiyoyin ilmantar da yara. Yayin da kuma za a ba da kulawa sosai ga raya al'adu da koyar da tarbiya ta gari ga matasa da yara a wannan yanki ba tare da karbar kudi ba.
A yayin shirin shekaru biyar a karo na 12, ma'aikatun kudi, da na ilmi na Sin sun hada gwiwa wajen aikin kafa cibiyoyin ilmantar da yara makarantun kauyuka. Sannan za a kebe kudi yuan biliyan 2.45 domin kafa cibiyoyin ilmantar da yara 8000 a wurare daban daban na Sin.(Fatima)