A Laraban nan 4 ga wata, aka yi taron harkokin albarkatun kwadago da ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma na jihar Xin Jiang, inda aka ba da labari cewa, jihar ta sami ci gaba sosai wajen tabbatar da tsarin ba da inshorar tallafin tsofaffi a kauyuka, wadda tana sahun gaba a nan kasar Sin. Kuma ta kasance jihar da ta tabbatar da wannan aiki kafin shekara daya a dukkan kasar.
Jami'in ofishin kula da harkokin albarkatun kwadago da ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma ya bayyana cewa, jihar ta gudanar da aikin gwaje-gwaje a wasu wurare game da ba da inshorar tallafin tsofaffi na kauyuka yadda a dukkan fannoni wanda ya shafi gundumomi da birane 92, kuma ya amfana masu aikin noma da masu kiwon dabbobi kimanin miliyan 4.65.
Yawan mutanen da suka sayi inshorar ya kai kashi 88 cikin 100, kuma yawan kudin inshorar da aka samar ya kai kashi 100 cikin 100.
Wannan jami'i ya yi bayanin cewa, jihar tana sahun gaba a kasar Sin wajen gudanar da aikin ba da inshorar tallafin tsofaffi a birane da garuruwa, a cikin shekarar da ta gabata, yawan mutane da suka sayi inshorar tallafin tsofaffi a birane da garuruwan jiyar ya kai dubu 200, kuma an samar da dukkan kudin insharar a karo na farko yadda ya kamata a wurare daban-daban.(Amina)