Bisa labarin da aka bayar, an ce, jimillar jarin da aka saka game da wadannan sabbin ayyukan sun wuce kudin Sin Yuan biliyan 458, cikinsu, ya zuwa yanzu, an kammala ayyukan da yawansu ya kai kudin Sin biliyan 70. Wadannan sabbin ayyukan da aka yi sun shafi harkokin wutar lantarki da kwal, da hako ma'adinai da harkar kirkire-kirkire, kuma masana'antun gwamnatin sun zama wani babban jigo ne dake taimakawa wajen raya jihar Xinjiang.
Bisa labarin da aka samu, an ce, a shekarar 2012, yawan sabbin ayyukan da masana'antun gwamnatin tsakiya ta Sin za su yi a jihar Xinjiang ya kai 178, kuma yawan jarin da za a saka ya kai kudin Sin RMB sama da biliyan 724.(Bako)