Rahoton ya nuna cewa, a shekara ta 2012, tattalin arzikin jihar Xinjiang ta samu farfadowa da bunkasuwa cikin sauri, kuma yawan karuwar GDP zai kai kashi 12 bisa dari a duk shekara. A shekara ta 2013, koma-bayan tattalin arzikin duniya da rashin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri za su haifar da tasiri ga tattalin arzikin jihar Xinjiang, amma duk da haka, bisa hasashen da aka yi, an ce, tattalin arzikin jihar zai ci gaba da habaka, wanda saurin karuwar zai zarce abin da aka yi a kan kasar Sin baki daya. Bisa hasashen, saurin karuwar GDP na jihar Xinjiang a shekara mai zuwa zai zarce kashi 12 bisa dari.
Wannan rahoto ya kuma yi hasashe da hangen-nesa game da abubuwan da za su haifar da tasiri ga tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma na jihar Xinjiang a shekara ta 2013, da kuma bayar da kyawawan shawarwari dangane da hakan.(Murtala)