An ba da labari cewa, ana kiran taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, an bude kofa daki, inda wakilan jama'a na jihar Xinjiang suke tattaunawa kan rahoton gwamnatin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi kwanan baya, ga manema labaru a wannan rana.
Game da tambayar da manema labaru suka mika masa na cewa, "ko matakin da 'yan ta'adda na ET suka yi zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasar Sin da ta Pakistan?" Sai Nuer Baikeli ya ce, ko da yake, an tabbatar da cewa, kungiyar ta'addanci ta ET na da alaka da kungiyoyin ta'addanci na kasashen dake makwabtaka da kasar Sin, amma gwamnatin Pakistan ta ba da sanarwa sau da dama na cewa, ta ki yarda da duk wani harin da aka kaiwa kasar Sin, kuma za ta kiyaye ikon mulki da babbar moriyar kasar Sin.
Ya kara da cewa, Sin na cimma matsaya daya tare da kasashen dake makwabtaka da ita kan batun yaki da ta'addanci. Ya kamata, kasashen daban-daban sun yi hadin kai game da wannan batu.
Nuer Baikeli , ya kara jaddada wajibcin tabbatar da halin da ake ciki a jihar Xinjiang. Ya ce, ya kamata, a gudanar da doka da shari'a ta yadda ya dace a dukkan fannoni. Ba zai yarda da ko wane mutum ya dauki matakin kawo cikas ga aikin gudanar da doka da shari'a ba. Kuma ba zai amince da duk wani mataki da za a dauka ba wajen kawo barakar kasar da tayar da zaune tsaye .(Amina)