A yayin bikin, mataimakin gidan rediyon kasar Sin Xia Jixuan ya bayyana cewa, jerin harkokin da suka shafi gasar "Xinjiang da nake daukar hotonta" sun yi amfani da kafofin watsa labaru na ketare wajen nuna wata Xinjiang ta hakika ga duniya, wadanda suka samu martani sosai daga masu duba shafin Intanet na gida da na waje. Ana fatan wadanda suka ci wannan gasar za su bayyana abubuwan da suka gani kuma suka ji ga dimbin mutane, domin a kara fahimtar jihar Xinjiang.
Hou Hanmin, shugabar ofishin watsa labaru na jihar Xinjiang a nata jawabin ta ce, gidan rediyon kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a cikin ayyukan yada labaru ga duniya. Wannan gasar da bangarorin biyu suka hada kai wajen gudanar da ita za ta samar da wata kyakkyawar dama wajen nuna hakikanin jihar Xinjiang da daga kwarjininta a duniya yadda ya kamata.(Kande Gao)