Alhamis din nan 15 ga wata, a Urumqi hedkwatar jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, an kaddamar da bikin nuna hotunan jihar Xinjiang da manema labaru musulmai suka dauka da kuma bikin zabar hotuna mafi kyau.
Gidan rediyon kasar Sin da ofishin yada labaru na jihar Xinjiang ne suka yi hadin kai domin jagorantar wannan biki.
Bisa gayyatar da aka yi musu, manema labaru masu kula da aikin daukar hotuna 14 ne daga kasashen 10 ciki har da Turkiya, Saudiyya, Najeriya, Indonesiya, Malasiya da sauransu suke halartar bikin.(Amina)