Da misalin karfe 9 na safiya agogon Sin, an gano gawawwaki 18 a mahakar ma'adinan dake tsakiyar unguwar Araltobe a yankin Xinyuan dake gundumar Ili ta kabilar Kazak, sai dai kuma har zuwa yanzu ana neman sauran mutune 10, in ji mai magana da yawun gwamnatin yankin yayin da yake wa manema labarai bayani.
Wannan bala'in dai ya faru ne da misalin karfe 12.30 na safiyar ranar jiya Talata 31 ga wata, lamarin da ya rutsa da ma'aikata 28 dake kwana a rumfar wurin hakar ma'adinan a wannan lokaci, kuma an gane cewa, ma'aikatan wurin ne sannan yawancin su, sun fito ne daga gundomomin Yunnan da Fujian sauran kuma mazauna garin ne, in ji mai magana da yawun gwamnatin yankin.
A wani labarin kuma, sanadiyar ruwan sama mai karfi da aka kwashe kwanaki biyu ana shekawa wanda ya yi sanadiyar ambaliyan ruwa sosai da kuma zabtarewar laka mutane 4 ne suka rasa rayukan su, sannan kuma ana kan neman sauran guda 10 a gundumar Yunnan dake kudancin yammacin kasar Sin, in ji jami'an da abin ya shafa, ya zuwa yanzu dai an zuba sojoji fiye da 600 don taimakawa wajen neman wadanda suka bace da kuma baiwa wadanda suka rasa gidajen su matsugunni. (Fatimah)