An yi bikin bude taro karo na uku na dandalin hukumomin kwararru na Sin da Afrika kuma bikin kaddamar da shirin hadin kai na 10+10 tsakanin Sin da Afrika a yau Litinin 21 a ga wata a nan birnin Beijing. Mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi ya halarci taron tare da ba da jawabi. Mutane fiye da 200 sun halarci taron, ciki hadda wakilan kwamitin kula da ragowar ayyuka game da dandalin, jakadun kasashen Afirka da ke kasar Sin, da masu ilmin Sin da Afrika.
A cikin jawabinsa, Yang Jiechi ya bayyana kyakkyawan fata ga taron, da ''shirin hadin kai na 10 + 10'' da aka fara tafiyar da shi.
Wakilin hukumar kwararru ta Sin da Afirka ya bayyana cewa, za a yi amfani da wannan shiri domin kara hadin kai tsakanin Sin da Afrika a fannin al'adu tare kuma da zurfafa hadin kai tsakaninsu nan gaba. (Amina)