in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan kasar Sin ya halarci dandalin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin biranen Sin da Afirka karo na farko
2012-08-27 19:21:01 cri

Yau ranar Litinin 27 ga wata, aka gudanar da dandalin hadin gwiwa tsakanin kananan gwamnatocin wurare na kasar Sin da kasashen Afirka karo na farko a birnin Beijing.

A bikin bude dandalin, mataimakin firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son cigaba da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kananan gwamnatocin biranenta da na kasashen Afirka don ci gaba yadda ya kamata, don haka a cikin shekaru biyar masu zuwa, bangarorin biyu, wato Sin da Afirka za su yi kokari tare domin kara yawan birane masu sada zumunci ninkin adadin yanzu.

Wakilai sama da dari uku daga kasashen Afirka da yawansu ya kai 39 sun halarci wannan dandalin, a cikin su har da mataimakin shugaban kasar Uganda, mataimakin shugaba na farko na kasar Burundi da shugabannin larduna da magajin birane sama da saba'in na kasashen Afirka daban daban kamar yadda wakilan kasar Sin mahalarta dandalin da suka zo daga ma'aikatu, larduna da birane daban daban fiye da dari bakwai suka halarta.

Kungiyar sada zumunci da kasashen ketare ta kasar Sin ta jagoranci wannan dandalin na tsawon kwanaki biyu mai taken "Kara hadin kai da samu bunkasuwa tare".

Za a fitar da "sanarwar Beijing game da hadin kai tsakanin kananan gwamnatocin Sin da Afrika karo na farko" a gun dandalin, da kuma yarjejeniyar kulla zumunci tsakanin biranen bangarorin biyu da kuma yarjeniyoyin hadin kai tsakanin kamfanonin bangarorin biyu. Za a gudanar da irin wannan dandali duk bayan shekaru biyu-biyu.(Amina&Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China