Babban sakataren dandalin raya hadin kan Sin da Afirka a bangaren masana'antu, wanda ya karbi bakuncin wannan taro, Mista Cheng Zhigang ya ce, wannan kawancen ya kasance wani dandalin cinikayya, wanda aka kafa shi don cin gajiyar albarkatun teku na kasar Sin da kasashen Afirka, bunkasa ciniki a tsakanin masuntan bangarorin 2, da kara azama ga hadin gwiwar da ake yi a tsakanin Sin da Afirka a fannin sun kifi a teku.
Ya ce, yadda aka kafa wannan kawance, zai taimakawa raya cinikayya da hadin kai a tsakanin bangarorin 2, da kyautata fasahohin da kasashen Afirka suke amfani da su a fannin kamun kifi, sarrafa albarkatun teku, gami da jigilarsu. Sa'an nan kawancen zai zama wata hanyar musamman da za a bi don yin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a sana'ar kamun kifi. (Bello Wang)