A ran 24 ga wata, wakilai mahalartar taron farko na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ta fuskar watsa labaru sun ziyarci gidan rediyon kasar Sin CRI. Ta yin amfani da wakoki da raye raye irin na Afirka kuma cikin harsunan Afirka biyar, CRI ta marabce su tare da mika masu gaisuwa hannu biyu biyu.
Wang Gengnian, shugaban CRI wanda yayi jawabi a yayin bikin maraba, ya ce, yanzu gidan radiyon CRI na yin amfani da harsunan Turanci da Faransanci da Larabci da harshen Portugal da Hausa da Kiswahili wajen watsa labaru ga abokai 'yan Afirka. Sannan kuma kawo yanzu , an kafa rediyo na zangon FM 20 a kasashen Afirka, ban da azuzuwan Confucius guda 3 da ake dasu, wadanda suka samu karbuwa daga masu sauraro dake Afirka. Hakan ,a cewar Wang Gengnian, ya samar da wani dandali ga Sin da Afirka wajen fahimtar juna.
Madam Concilie Nibigira, ministar sadarwa da watsa labaru ta kasar Burundi ta bayyana a lokacin cewa, ta wannan ziyara, an gano babban ci gaban da CRI ya samu. Musamman yadda aka riga an maida ayyukan rediyo da talabijin a kasar Sin zuwa na zamani don haka kafofin watsa labaru na kasashen Afirka suma suna yin kokari a wannan fanni.(Kande Gao)