in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan yin kokari tare da Afrika don raya dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi
2012-08-28 17:22:41 cri
A yau 28 ga wata, a nan birnin Beijing ne, aka rufe taron tattaunawar hadin gwiwa karo na farko tsakanin matakai daban daban na gwamnatocin kasashen Sin da Afrika, mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin Dai Bingguo ya halarci taron, tare da yin jawabin cewa, a aikin sabon yanayin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da abokai kasashen Afrika, don samun ci gaba da sabbin kirkire-kirkire, da karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da inganta hadin gwiwa a fannonin daban daban tsakaninsu, kana da ingiza dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

Dai Bingguo ya jaddada cewa, hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin matakai daban daban ya zama wani muhimmin bangare cikin dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma a gun taron, mahalartar taron sun tattauna sosai game da taken taron "Inganta hadin gwiwa tsakanin yankuna daban daban na kasar Sin da kasashen Afrika, don sa kaimi ga samun bunkasuwa", kuma bangarorin biyu sun cimma daidaito a fannoni da dama, abin da ya kai ga samun sakamako mai gamsarwa.

Haka kuma a gun bikin rufe taron, an fitar da sanarwar Beijing ta taron, sannan an daddale yarjejeniyoyin kulla dangantakar sada zumunta tsakanin larduna da jihohi na kasashen Sin da Afrika.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China