in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai yiwuwar ganin ciniki tsakanin Sin da Afrika ya kara hauhawa
2012-12-27 20:27:39 cri
Akwai yiwuwar cewa, cinikayyar tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin za ta kai wani matsayin koli a wannan shekara sakamakon wani tsarin ciniki mai armashi, inji ma'aikatar ciniki ta kasar Sin a ranar Alhamis 27 ga wata.

Cinikayya tsakanin nahiyar ta Afrika da kasar Sin ta kai kudin dalar Amurka biliyan 163.9 a farkon watanni 10 na wannan shekara, abin da ya haura da kashi 20 a cikin 100 a shekaru a jere.

Girman ciniki da Afrika ya tsaya ne a kashi 14 a cikin 100 fiye da na matsakaicin yanayi, inji ma'aikatar.

Sin ta ba da rangwamen kudin jigila da kashi 60 cikin 100 na kayayyakin da ta shigo da su daga kasashen Afrika 30 tun farkon watan Janairun wannan shekara domin ba da kwarin gwiwwa wajen inganta kasuwanci da nahiyar.

Tsarin zuba jari kai tsaye ba tare da neman tallafin kudi ba a nahiyar ya kai dalar Amurka biliyan 1.5 a tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban bana, abin da ya haura da kashi 17 cikin 100 na shekarar bara.

Fiye da masana'antun kasar Sin 2000 ne suke hulda da nahiyar ta Afrika a fannin zuba jari a fannin aikin gona, sadarwa, makamashi, da bangaren dafe-dafen abinci. Haka kuma Afrika a yanzu haka ita ce kasuwa mafi girma na biyu wajen samar da ayyukan yi na kwangila ga kasar Sin. Ma'aikatun kasar Sin sun saka hannu a kan yarjejeniyar kwangiloli na kimanin kudi dalar Amurka biliyan 38.2 tsakanin su da abokan huldarsu na Afrika a watannin Janairu da Oktoban bana, abin da ya haura da kashi 27 cikin 100 a shekaru a jere.

Ayyukan kwangilan galibinsu sun hada da samar da ababen more rayuwa kamar su hanyoyi, gadoji da tashoshin jiragen ruwa, sannan kuma akwai ayyukan gina wajen adana ruwa da kuma ayyukan samar da wutar lantarki.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China