Long Ling ya ce, yayin da ake samun bunkasuwar tattalin arziki a kasashen Afirka, za a kara samun dama da kuma fuskantar kalubale kan hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kana za a fadada wannan hadin gwiwar sannu a hankali. Ya zuwa watan Yuni na bana, yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya kai dala biliyan 145. Yawan jarin da Sin ta zuba kai tsaye ya kai dala biliyan 15 na wannan adadi.
An kafa tsarin gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a ranar 10 ga watan Nuwanba na shekarar 2010, inda aka gudanar da karo na farko a nan birnin Beijing. Ana gudanar da taron ne a kowace shekara don inganta aiwatar da ayyukan nan gaba da aka tsara a gun dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da ake gudanarwa shekaru uku-uku. Wannan taro wani muhimmin dandali ne na yin mu'amala a tsakanin kamfanonin Sin da kasashen Afirka. (Zainab)