Mista Liu ya ce, tun bayan da kasar Sin da kasashen Afirka suka kulla sabuwar huldar abota da ta shafi manyan tsare tsare a shekarar 2006, bangarorin 2 sun tsaya kan zama daidaiwa daida da imani da juna a fannin siyasa, da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki domin amfanawa juna, da musayar ra'ayi a fannin al'adu, tare da cimma nasarori da yawa a hadin gwiwar da suke yi a wadannan fannoni.
Saboda haka in ji shi ana fatan ganin bangarorin 2 wato kasashen Afirka da kasar Sin za su yi amfani da wannan dama domin kara mu'amala da daidaita ra'ayoyinsu, da zurfafa hadin kan kafofin watsa labarai nasu, ta yadda za a iya taimakawa kara sanin juna da zumunci, da sa kaimi ga hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin.
Shi ma Jean Ping, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU mai barin gado, da wakilan kasashe daban daban dake nahiyar Afirka, wadanda suka halarci ganawar, sun nuna yabo kan sakamakon da aka samu a wajen dandalin da ke gudanarwa.
A ganinsu, hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen Afirka dole ne za ta taka muhimmiyar rawa wajen raya sabuwar huldar abota da ta shafi manyan tsare-tsare a tsakanin bangarorin 2. (Bello Wang)