Sin ta yi maraba ga yadda bangarorin da ke rikici a Afrika ta tsakiya suka amince da yin shawarwari cikin lumana
Game da yadda bangarorin dake rikici a kasar Afrika ta tsakiya, suka amince da yin shawarwari don shawo kan wannan matsala a birnin Libreville na kasar Gabon, kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ranar 7 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin na adawa da farmakin da dakarun da ke adawa da gwamnatin da su kaiwa a kasar, tare da nuna goyon baya ga kokarin da kungiyar AU da kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika da kasashen da abin ya shafa suka yi domin warware rikicin, haka kuma kasar Sin na yi maraba da yadda bangarorin dake gaba da juna na kasar suka amince da yin shawarwari cikin lumana.
Haka kuma, Hong Lei ya ci gaba da bayyana cewa, yana fatan bangarorin za su maida hankali kan raya kasarsu cikin lumana da kiyaye cikakken yanki da mulkin kan kasar, kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen duniya, don taimakawa Afrika ta tsakiya wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Bako)