Bisa labarin da aka samu, an ce, wadannan kamfanoni na kasar Sin hudu sun hada da reshen kamfanin motar Yiqi, da ke zuba jari a Afirka, kamfanin zuba jarin Huachen na Sin da Afirka, reshen kamfanin motar Qirui da ke kula da harkokin zuba jari a ketare, da kuma kamfanin motar arewancin Sin, bisa hasashen da aka yi, gaba daya yawan motocin da za su samar a Afirka zai kai dubu 100, da suka hada da motocin fasinjoji, manyan motocin daukar kaya, da dai sauran motocin sufuri da za su samar ta fasahar kasar Sin.
A shekarar 2006, bankin raya kasar na Sin ta kafa asusun ba da lamuni na Sin da Afirka bisa tsarin da aka fitar, yayin dandalin taron hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, haka nan asusun na zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka, ta hanyar zuba jari ga kamfanonin hada hadar hannayan jari, da kuma sa kaimi ga karin kamfanonin Sin, domin su habaka ayyukansu a Afirka.
A halin yanzu, asusun na da darajar kudaden da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan 3, kuma ana sa ran adadin zai karu zuwa dallar Amurka biliyan 5 a nan gaba. (Maryam)