in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin ya gana da ministan harkokin wajen Faransa
2013-04-12 20:17:17 cri
Ranar 12 ga wata, Yang Jiechi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin ya gana da Laurent Fabius, ministan harkokin wajen kasar Faransa da ke ziyara a nan Beijing, fadar gwamnatin kasar Sin, inda suka jaddada wajibcin ci gaba da inganta huldar da ke tsakanin kasashen 2.

A yayin ganawar, Yang Jiechi ya ce, ya kamata kasashen 2 su ci gaba da yin tattaunawa a tsakaninsu don samun amincewar juna, ta yadda za su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu dangane da al'amuran kasa da kasa.

Shi ma a nasa bangaren, mista Fabius ya bayyana fatansa na kyautata mu'amala a tsakanin manyan jami'an kasashen 2 da tattaunawa ta fuskar siyasa, da habaka hadin gwiwa, da kara azama kan yin mu'amala ta fuskar al'adu, a kokarin raya huldar da ke tsakanin Faransa da Sin daga dukkan fannoni. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China