A wata ganawar da manema labaru yayin taron majalisa na shekara- shekara, Yang ya ce yana fatan dukkan bangarori za su dau kawance tsakanin Sin da Afirka cikin adalci kana za su mutunta ra'ayin Afirka na zabin abokan hulda da kansu.
Ya kuma yi kiran karin musaya, rage rashin yarda da kuma zargi ga batun hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kana a yi hadin gwiwa a fuskantar bunkasa zaman lafiya daidaito da kuma ci gaba a Afirka.
Ya ce kasashe da dama suna kara bunkasa dangantaka tsakaninsu da Afirka kuma Sin na mai maraba da irin wannan hadin gwiwa.
Ya ci gaba da cewa hadin gwiwa ta musamman na ci gaba da bunkasa a shekaru da suka wuce kuma bangarorin biyu suna aiwatar da matakai da aka cimma a taron ministoci karo na biyar na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.
Yang ya kara da cewa Sin da Afirka za su kara kaimi a fuskar zuba jari da samar da kudade, ba da tallafi, hada kan kasashen Afirka, musaya tsakanin farar hula, da ma zaman lafiya da tsaro.
Ya ce hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ya dace da burin jama'a na cimma dorewa da bunkasa a kasashensu, da kuma hadin kai tsakanin kasashen Afirka gami da adalci a tsarin kasa da kasa.
Da kuma yake amsa tambayoyi kan dangantaka tsakanin Sin da kasashen yankin Latin na Amurka. Yang ya ce Sin tana mai da hankali ga kafa kyakkaywar dangantaka da kasashe dake yankunan Latin da Karibiyan na Amurka.
Ya ci gaba da cewa Sin a shirye take ta hada kai da dukkan yankuna kamar na Latin da Karibiyan da ma kafa wani dandalin hadin kai tsakanin yankin Latin na Amurka da kasar Sin. (Lami Ali)