Li Keqiang ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar Afirka ta tsakiya, Francois Bozize dake halartar bikin kaddamar da dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Larabawa a karo na 3.
Li Keqiang ya lura cewa, kamfanonin kasar Sin da dama sun zuba jari a kasar Afirka ta tsakiya a fannonin aikin gona, amfanin albarkatu da dai sauransu. Kuma ta haka bangarorin biyu sun fadada hadin gwiwarsu, wanda ya kara azama ga jama'ar kasashen biyu da su samu fahimtar juna, da kuma aza tubali kan hadin gwiwarsu a tsakanin jama'ar kasashen biyu.
A nasa bangaren shugaba Francois Bozize yan yi fatan kasashen biyu za su zurfafa hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki, zamantakewar al'umma da dai sauransu bisa tushen fahimtar juna, da gaggauta yin hadin gwiwa kan aikin gona, ayyukan more rayuwa, da ma'adinai wanda ta haka za a inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)