Bisa labarin da kafar yada labarai ta kasar Amurka ta bayar a ran 14 ga wata an ce, Amurka ta riga ta tasa keyar wani kusa a kungiyar Al-Qaeda zuwa kasarta domin yi masa hukunci, wanda da farko aka tsare shi a kasar Lybia, bisa tuhumarsa da laifin shirya aiwatar da hare-hare.
Jaridar Washington Post ta ba da labari cewa, wani jami'in da bai fayyace sunansa ba ya ce, watakila za a yanke masa hukunci a ran 15 ga wannan wata.
Wannan kusa mai suna Abu Anas Al-Libi mai shekaru 49 a duniya, an haife shi a kasar Lybia, kuma ya taba yi amfani da sunan Nazih Abdul-Hamed Nabih al-Ruqai'i.
Kasar Amurka tana zargin shi da laifin aiwatar da jerin hare-hare kan Amurkawa a fadin duniya, lamuran da haddasa mutuwar mutane da dama, ciki har da rasuwar mutane 224 a cikin harin da ya aiwatar a ofishin jakadancin kasar Amurka dake Tanzaniya da Kenya. (Amina)