Shugaban majalisar dattawan Najeriya mista David Mark, dake magana a babban birnin tarayya Abuja, ya kimanta wannan hari da rashin imani, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla biyar. Haka kuma ya kara da cewa kai hari a wani wurin ibada wani mummunan aiki ne.
Haka zalika mista David Mark ya yi kiran al'ummar kasar baki daya da ta ci gaba da ba da hadin kai kamar yadda ta saba ga jami'an tsaro da bayanai da su taimakawa ga kawar da ayyukan kungiyar Boko Haram.
Sannan kuma ya yi kira ga shugabannin dake da hannu kan wadannan kashe-kashen mutane da su yi watsi da hanyar da suka dauka domin amincewa da yin shawarwari.
A kalla mutane biyar suka mutu, hada dan kunar bakin waken, yayin da wasu shida suka ji mugun rauni a lokacin harin, a cewar hukumomin sojojin Najeriya a ranar Jumma'a. (Maman Ada)