'Yan sandan sun ce, a labarin da suka samu daga gwamnatin Somaliya, sojojin gwamnatin Somaliya sun hallaka 'yan ta'adda biyu a wata tashar binciken ababen hawa da ke Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, kuma daya daga cikinsu Fazul Abdullah Mohammed ne. A cewar 'yan sandan, suna hada kai da sassan tsaro na Somaliya, domin samun karin bayani. Bayan haka, suna kuma kokarin binciken kwayar halitta ta DNA da suka dauka daga gawawakin biyu.
A dai wannan rana, babban mai ba da shawara ga firaministan kasar Somaliya, Abdirahman Omar Osman ya tabbatar da mutuwar Fazul Abdullah Mohammed, wanda karo na farko ne da wani jami'in gwamnatin Somaliya ya amince da harbe shi da sojojin gwamnati suka yi, kana a cewarsa, gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya na farin cikin sanar da hallaka daya daga cikin manyan shugabannin 'yan ta'adda a duniya, kuma nan gaba, za ta ci gaba da hada kai da kasa da kasa, a kokarin yakar ta'addanci.(Lubabatu)