Kakakin kungiyar ta'addanci ta 'yan kaifin kishin Islama ta kasar Mali Sed Ould Bu Mama, ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Mauritania ta wayar tarho a ran 17 ga wata cewa, kungiyarsa ta mika wuya ga sojin kasar Aljeriya.
Yayin zantawar, Sed Ould Bu Mama ya nuna cewa, an yi masa kisan kai a ran 16 ga wata, amma bai yi karin bayani kan lamarin ba. Sed Ould Bu Mama, ya nemi shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz, da ya yi iyakacin kokarin tasa keyarsa zuwa kasar Mauritania don a hukuta shi a can, ganin cewa shi dan kasar ta Mauritania ne.
An ba da labari cewa, Sed Ould Bu Mama, ya zama kakakin kungiyar 'ya kaifin kishin Islama ne, tun lokacin da kungiya 'yan tsattsauran ra'ayin kishin Islama ta mamaye yankin arewacin kasar Mali. (Amina)