in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaro a Nigeriya sun harbe wassu mutane biyu da ake zargin 'yan kungiyar ta'adda ne
2012-08-01 10:02:05 cri
A jiya Talata 31 ga wata rundunar tsaro ta hadin gwiwwa a jihar Borno dake arewa maso tsakiyar kasar Nigeriya sun ce sun harbe wassu mutane biyu da ake zargin mambobin kungiyar 'yan ta'adda ne a unguwar Monguno.

Laftanar kanar Sagir Musa kakakin rundunar ya sheda ma manema labarai a garin Maiduguri, babban birnin jihar cewa a lokacin wannan harin sun samu karbe makamai masu dimbin yawa.

Kanar Musa ya bayyana cewa, mutanen biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne suna raka wannan tulin makaman ne lokacin da suka rutsa da su a musayar wuta da suka yi ne ya yi sanadiyar mutuwar wadancan.

Makaman da aka samu sun hada da bindigogin roka 8, da bam na amfani da shi ma bindigar roka 10 da na'uran chargin bindigar rokar 10. Sai kuma manyan bindiga kirar AK-47 2 da jakkunan albarusai da harsasai 13.

A cewar sa wadannan makamai an boye su ne a cikin wata shudiyar mota kirar Tayota Hilux a kan hanyar zuwa Maiduguri. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China