in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta wargaza wata cibiyar Alqa'ida dake aikawa da mutane zuwa yin fada a Mali
2012-11-25 16:15:26 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Morocco a jiya asabar24 ga wata a Rabat babban birnin kasar ta sanar da cewa ta wargaza wata cibiyar dake da alaka da kungiyar Alqa'ida wanda ke aikawa da mabiyan ta zuwa kasar Mali da yankin Sahel domin taimaka masu wajen yin fada.

Wannan cibiya tana aiki ne ta hanyar bada horo da kuma diban matasan kasar Morocco masu ra'ayin kungiyar ta Alqa'ida domin aika wa da su yin yaki a karkashin sunan yin jihadin addini a yankin sahel na Afrika,kamar yadda sanarwa ta yi bayani.

Wannan cibiya dai tana aiki ne daga garuruwan Nador, Casablanca, Guercif, Laayoune da Kalaat Sraghna inji sanarwar wanda ya kara da cewa a kalla mutane 20 ne aka rigaya aka aika da su domin yin fada tare da Alqa'idan a karkashin kungiyar AQIM da wassu sauran kungiyoyin da ke alaka da juna a yammacin Afrika, saura kuma an aika dasu kasar Libya.

Arewacin Mali dai 'yan tawaye sun karbe shi sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar 22 ga watan Maris na bana, abin da ya haifar da tsoron AQIM da kuma sauran kungiyoyin masu aikata fataucin miyagun kwayoyi da mutane, ganin cewa za su yi ta cin karen su babu babbaka a yankin dake kudancin gabar Hamadar sahara.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China