A cikin harin farko, jirgin ya kai hari a zauren taron 'yan kungiyar ta Al'Qaida a cikin arewacin yankin Jaar da ya kasance karkashin kungiyar tun cikin shekarar da ta gabata. Wannan hari ya yi sanadiyar mutuwar 'yan kungiyar guda 10, kamar yadda hukumomi yankin da ba su yarda aka baiyan sunayensu ba suka sanar ma kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin.
Shugaban 'yan kabilar yankin ya sanar da cewa, yana tsammanin jagororin 'yan kungiyar guda biyu sun mutu a cikin wannan hari.
A cikin hari na biyu da aka kai ga wata mota ta 'yan kungiyar a Haroor da ke kusa da Jaar, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 da ke cikin motar kamar yadda kafar gwamnatin kasar ta sanar.
Mazauna a yankin na Jaar sun sanar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da cewa, jiragen soji na ci gaba da shawagi a Jaar.
Har yanzu dai kungiyar Al-Qaida ba ta yi wani tsokaci ba kan wannan hari na baya-baya da aka kai mata. Dakarun kasar Yeman da ke samun goyon bayan dakarun kasar Amurka, suna ci gaba da kai hare-hare ga sansanonin kungiyar Al-Qaida a cikin yankunan kudanci a matsayin wani mataki na kawar da aikin ta'adanci daga yankuna a cikin shekara guda ta rikicin siyasar kasar Yeman. (Abdou Halilou)