Babban sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya yi tir da allawadai da babbar murya kan hare haren ta'adancin da aka kai wa wasu coci biyu dake birnin Garissa na kasar Kenya, wanda a cikinsu akalla mutane 17 suka mutu.
"Wadannan hare hare da gangan dake shafar wuraren ibada, aikata laifi ne kuma da ya kamata a hukunta", in ji mista Ban a cikin wata sanarwar da kakakinsa ya karanta.
"Babu wata hujjar da za'a bada na kai hare hare kan fararen hula da basu ji, basu gani ba. Mutanen da suka kai wadannan hare hare da ma kuma wasu hare haren ta'adanci na baya baya da aka kai a kasar Kenya ya kamata a sanyasu cikin manyan laifuffuka", in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)