Wannan jami'in da ba ya son bayyana sunansa ya ce, an kashe Rahman ne a Waziristan dake arewa maso yammacin Pakistan, amma bai yi karin bayani ba dangane da rasuwarsa.
A baya akwai rahotannin dake nuna cewa, wani jirgin saman hukumar leken asirin Amurka wanda ba matuki a cikinsa ya kai hari a wannan wuri. Kawo yanzu dai ba'a san ko akwai wata alaka tsakanin mutuwar Rahman da wannan hari ko a'a.
An ce, Atiyah ABD Al-Rahman, dan asalin kasar Libya ne, wanda ya zama jagora na biyu na kungiyar Al Qaida bayan da aka kashe Osama bin Laden, haka kuma shi ne babban na hannun daman Ayman al-Zawahiri, jagoran kungiyar Al Qaida.
A shekarar da ta gabata, akwai rahoton da ya bayyana cewa Rahman ya mutu, amma gwamnatin Amurka da kungiyar Al Qaida ba su tabbatar da gaskiyar rahoton ba.(Murtala)