Onitiju ya bayyana hakan ne ga manema labaru ranar Asabar 9 ga watan nan a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno, yana mai cewa rundunar sojin zata kafa wani kwakkwaran kwamitin bincike, da zai nazarci zargin da ake wa wadanda rundunar ke tsare da su, don gane da kai hare-hare, da kisan mutane a yankunan kasar daban-daban.
Mataimakin daraktan yace tawagar rundunar ta ziyarci garin Maiduguri ne, domin saduwa da dukkanin masu ruwa da tsaki, dama shuwagabannin al'umma, da nufin karfafa dangantaka, da neman hadin kan su, ga bukatar sake maido da kyakkyawan yanayin zamantakewa a jihar, dama ragowar yankunan dake arewacin kasar.
Daga nan sai ya musanta zargin da akewa jami'an rundunar, na kashe wasu daga manbobin kungiyar ta Boko Haram, yana mai cewa dakarun soji, na aiki ne domin dawo da managarcin yanayin zaman lafiya, bawai kisan farar hula ba. (Saminu Alhassan Usman)