Ofishin jakadancin Amurka dake kasar Kenya ya gargadi a ranar Asabar cewa akwai alamar samun harin ta'adanci a birnin tashar ruwan kasar Kenya na Mombasa, tare da yin kira ga 'yan asalin kasar Amurka da su kiyaye zuwa wannan birni har zuwa ranar daya ga watan Yuli. Wannan gargadi ya biyo bayan kwanaki uku bayan kama wasu 'yan kasar Iran dake dauke da sinadarin kera bam.
Game da wannan lamari tuni hukumomin kasar Kenya suka karfafa matakan tsaro a Mombasa da kudu maso gabashin kasar, da kuma muhimman wurare a cikin kasar, bayan wannan hannunka mai sanda na kasar Amurka na yiyuwar kai hare haren ta'adanci. Babban komanda na 'yan sandar kasar Kenya na wannan yanki, Aggrey Adoli ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na kan ko ta kwana. "Mun samu labarin cewa akwai yiyuwar hare hare, dan haka jami'an tsaro a shirye suke domin kawar da duk wani harin ta'adanci." ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho. (Maman Ada)