Kwamishinan 'yan sanda na jihar Filato Christian Olakpe ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Jos, babban birnin jihar bayan wata ganawar tsaro ta gaggawa da aka gudanar a ranar Jumma'a.
Bugu da kari ya bayar da sanarwar haramta sayarwa ko amfani da abubuwan fashewa a matsayin matakan da aka dauka na gudanar da bikin Kirsimetin wannan shekara lami lafiya.
Har ila yau, kwamishinan 'yan sandan, ya bukaci al'ummar jihar da su taimakawa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da bayanai masu muhimmanci don zakulo bata gari da ke da niyyar kawo kafar ungulu a bikin a jihar.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, za a karfafa sintirin tsaro a wuraren da ke bukatar tsaro a jihar da kwanakin baya ta fuskanci matsalar tsaro, kashe dubban wadanda ba su ji ba su gani ba, ciki har da 'yan majalisun dokoki biyu da aka kashe a watan Yulin da ya gabata.
Don haka, ya bukaci al'ummar jihar, da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, domin an girke jami'an tsaro cikin shirin kota-kwana yayin da kuma bayan shagulgulan na kirsimeti. (Ibrahim)