Kaftin Mustapha Salisu, kakakin rundunar sojoji na musammun ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa sojojin kasar za su kai wani samame a wasu kauyuka na wannan jihar dake fama da tashe-tashen hankalin dake salwantar da rayuka.
Za'a gudanar da wannan aikin soja, dalilin wasu hare haren kwana kwanan nan da wasu mutane masu dauke da makamai da suka kai kan wasu yankunan jihar.
An yi fama da ruruwar tashe-tashen hankali a makon da ya gabata a cikin wannan jiha, inda wasu 'yan majalisa biyu suka bakunci lahira a ranar Lahadin da ta gabata a cikin wani harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a yayin wani bikin jana'iza, haka kuma a kalla mutane 90 suka mutu a cikin wasu hare-haren baya baya tun daga ranar Jumma'ar da ta gabata da yamma.
A cikin sanarwar da aka fitar ranar Asabar 14 ga wata Yuli, rundunar kasar ta gargadi mazauna yankunan dake kusa da jihar da su kwantar da hankalinsu, da yin taka tsantsan da kuma kaucewa zuwa wuraren da sojojin kasar za su kai samame har zuwa wani lokaci. Tare yin kira da ga al'ummomin yankunan da su ba da hadin kai ga sojojin kasar ta hanyar taimaka musu da bayanai. (Maman Ada)