A cikin wani sakon text da aka aikawa Xinhua, majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, an gano wasu gawawwaki 50 da aka kona a safiyar ranar Lahadi a majami'ar COCIN a kauyen Matsai.
Wakilan Xinhua da ke birnin Jos da ake tashin hankali, sun ce an kashe mutane 20 a ranar Lahadi da rana yayin da ake jana'izar wadanda suka rasa rayukansu a harin ranar Lahadi, ciki har da dan majalisar dattawa Gyang Dantong da ke wakiltar Filkato ta arewa da shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Gyang Fulani.
Kafin kisan nasa a ranar Lahadi, marigayi Fulani ya shaidawa Xinhua a ranar Asabar cewa, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kashe mutane a kalla 20 a ranar Jumma'a da dare a Barikin-Ladi, inda suka mamaye kauyukan da ke yankin.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana fita a wasu kananan hukumomi hudu da ke jihar ba tare da wani bata lokaci ba.
Yankunan kananan hukumomin da dokar ta shafa, sun hada da ,Jos ta kudu, Jos ta arewa, Barikin-Ladi da Riyon.
Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kwamishinan watsa labarai na jihar Abraham Yiljap ta ruwaito gwamnan jihar Jonah Jang a ranar Lahadi yana cewa, sanya dokar ta zama waijibi bisa la'akari da tabarbarewa tsaro a jihar. (Ibrahim)