Babban masanin tattalin arziki mai kula da harkokin kasuwannin kasa da kasa na bankin CIBC na kasar Canada Mr Peter Buchanan ya shedawa manema labaru a kwanan baya cewa, ya zuwa yanzu, babu alamar da ta nuna cewa, Sin za ta dauki kwararen matakai don rage saurin karuwar tattalin arzikin kasar cikin gajeren lokaci ba, irin zancen da wasu mutane suka yi game da wannan matsala ba shi da tushe.
Peter Buchanan ya kara da cewa, manufofin da gwamnatin kasar Sin ta fitar ciki hadda samar da guraben aikin yi da kuma kara bunkasuwar sha'anin ba da hidima da gidaje za su gaggauta bunkasuwar tattalin arziki nan gaba. Ban da haka, farfadowar tattalin arzikin Amurka da Turai zai taimakawa kasar Sin wajen fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje. (Amina)