in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ribar Masana'antu a Sin ya haura zuwa 6.3 cikin dari a watan Yuni
2013-07-27 16:29:04 cri

Manyan masana'antun kasar Sin sun samu haurawar ribarsu da kashi 6.3 cikin dari na shekara shekara a watan Yuni, inda hakan ya nuna koma baya daga kashi 15.5 cikin dari na watan Mayu, kamar yadda alkalumma daga hukumar kididdigar kasar suka nuna ranar Asabar 27 ga wata.

Masana'antu da kudaden shigarsu yake kaiwa sama da Yuan miliyan 20 wato daidai da dalar Amurka miliyan 3.24, ya haura zuwa yuan biliyan 502.42, inji bayani da hukumar kididdiga ta kasar ta samar.

A cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, yawan ribar da suka samu ya karu da kashi 11.1 cikin dari, har ya kai Yuan trillion 2.58 daidai da dalar Amurka biliyan 418.75, inda shi ma ya yi kasa daga kashi 12.3 cikin dari da aka samu a watanni biyar na farkon bana.

Dalilin koma bayan da aka samu a watan Yuni shi ne saboda bunkasar harkokin cinikayyar ya yi kasa, ga kuma tsada kana da haurawar ma'auni da aka saba yi shekara shekara, inji Hi ping, wani manazarci na hukumar kididdigar.

Binciken ya nuna cewa, kafofi masu zaman kansu su ne suke kan gaba inda suka samu ribar kashi 15.8 cikin dari a farkon rabin shekarar bana, kana cibiyoyi mallakar gwamnati su ma nasu ribar ya kai kashi 4.8 cikin dari a wannan lokaci, bisa bayani da hukumar kididdigar ta kasa ta samar.

Daga cikin masana'antu 41 da aka duba, guda 30 sun samu bunkasa a riba a watanni shidan farko na shekarar, sannan guda 8 sun samu koma baya a ribar da suke samu.

Sassa guda uku na hakar kwal, karafa da narka karafan duka sun samu koma baya a riba da suke samu.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China