Bisa ga bayanai da mai dumi-dumi da aka gabatar, an ce, a watan Febrairu da ya gabata, alkaluman sayen kayayyaki da ke nuna ingancin tattalin arziki a bangaren masana'antu, wanda aka fi sani da PMI, ya ragu da kashi 0.3 cikin dari bisa na makamancin lokaci na watan jiya, wato kashi 50.1 cikin dari. Watanni biyu a jere ke nan alkaluman PMI bai kai yadda ake zato ba. Hakan ya nuna cewa, bangaren masana'antun kera kayayyaki ya dan samu farfadowa ne kawai ba kamar yadda ake zato ba.
Ko da yake bisa bayanan da mahukuntan kasar Sin suka bayar, an ce, alkaluman PMI yana nuna alamar karuwa, amma watanni 2 a jere ya dan ragu, wannan na nuna cewa, alkaluman yanayin tattalin arziki na kasar Sin sun sake raguwa zuwa kashi 50 cikin dari.
A ganin Yang Hongxu, mataimakin shugaban kwalejin nazarin harkokin kadarori na Yiju na birnin Shanghai, yanzu kasar Sin ta dan farfado da tattalin arzikinta.(Tasallah)