Ya zuwa yanzu, adadin na ta karuwa daga kashi 7 bisa dari, zuwa kashi 8 bisa dari cikin zango 5 na shekarar da muke ciki, don gane da hakan, masanan tattalin arziki suna ganin cewa, wannan mataki ba wai kawai zai samar da karin bunkasuwa ba ne, har ma zai iya samar da guraben aikin yi da kuma yin gyare-gyare a kasar.
Yayin taron manema labarai da aka kira a wannan rana, kakakin hukumar kididdigar ta kasar Sin Sheng Laiyun, ya bayyana cewa a halin yanzu, ana gamuwa da kalubale ta fuskar yanayin tattalin arzikin kasa, don haka a nan gaba, za a ci gaba da bunkasa tattalin arziki, tare da kuma yin gyare-gyare a kasar, ta yadda za a iya karfafa yanayin tattalin arziki a kasar ta Sin. (Maryam)