in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aunin karuwar farashin kayayyaki ya karu da 2.7 cikin 100 a Yuli
2013-08-09 20:42:57 cri

Ma'aunin kididdigar farashin kayayyakin na kasar Sin ya nuna haurawa sama inda ya tashi zuwa kashi 2.7 a cikin 100 a jere cikin shekara daya a watan Yulin nan, inda kuma ya tsaya cak a kan inda yake bai motsa ba a watan Yunin, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta nuna.

Adadin ya yi kasa da yadda kasuwa take sa rai na kashi 2.8 a cikin 100, kuma ta gasa cimma zaton gwamnati na kashi 3.5 a cikin shekarar duka.

Hukumar kididdiga ta kuma danganta wannan hauhawar galibi a kan farashin kayayyakin abinci da ya ci gaba da tashi a cikin shekarar gaba daya, abin da ya kai har kashi 5 a cikin 100 a watan Yuli. farashin kayayyakin abinci dai ya dauki kashi daya a cikin uku na lissafin ma'aunin kididdiga na kasar.

Yu Qiumei, wata babbar jami'iya a hukumar ta ce farashin kayayyaki na kasar ya samu tsayuwa cikin daidaito, idan aka kwatanta shi da na wata wata, ma'aunin watan Yuli ka karu da 0.1 a kan na watan Yuni kuma farashin kayayyakin abinci a watan Yuli ya tsaya cak bai motsa ba idan aka kwatanta dana watan baya.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China